Kotun daukaka kara a Najeriya ta bai wa hukumar INEC izinin sake saita na’urar zabe ta BVAS da aka yi amfani da ita yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da ya gudana a ranar 25 ga watan da ya gabata.
Yayin zaman kotun na ranar laraba a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, zaman da ya gudana karkashin jagorancin alkalai 3 da suka hadar da mai shari’a Joseph Ikyegh da ya karanto hukuncin kotun wanda ya sahalewa INEC saita na’urar ta BVAS gabanin zaben gwamnoni da ‘yan Majalisun jihohi da ke tafe a karshen makon nan.
Kotun ta umarci INEC ta nadi bayanan da ke cikin na’urar ta BVAS tare da adana su a waje mai tsaro baya ga sanya kwafi a rumbunan adana bayananta.
Read Also:
Kafin hukuncin na yau dai, Kotu ta baiwa dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP wato Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar LP damar gudanar da bincike kan na’urar da sauran kayakin zabe masu muhimmanci don samun hujjojin da suke ikirarin an tafka magudi a babban zaben kasar.
‘Yan takarar jam’iyyun adawar da suka zo na biyu da na uku a zaben shugaban kasar na Najeriya wanda Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara, sun bukaci isa ga na’urorin zaben ne don tattara hujjoji bayan shigar da karar da ke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar.
Sai dai bayan izinin isa ga na’urorin da kotun sauraren karakin zaben Najeriya ta bai wa ‘yan takarar jam’iyyun adawa, INEC ta daukaka kara kan hukuncin bisa kafa hujjoji da illar da hakan zai yi ga zaben Gwamnoni da ke tafe.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 37 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 18 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com