Sha’aban Sharada ya taya Abba gida-gida murnar lashe zaɓe

Dan takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jam’iyyar ADP Sha’aban Ibrahim Sharada ya taya zaɓaɓɓen gwamna jihar Abba Kabir Yusuf murnar lashe zaɓe.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa Facebook, Sha’aba Sharaɗa ya yaba wa hukumar INEC da cewa ta yi abinda ya kamata.

Da safiyar ranar Litinin ne hukumar zaɓen jihar ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri’u mafi rinjaye.

Sha’aban Ibrahim Sharada na jam’iyyar ADP ya samu ƙuri’a 9,402 a zaɓen da aka gudanar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com