Fadar Shugaban Kasa ta yi Martani Kan Batun Mika Mulki ga Tinubu
Garba Shehu ya ce shirin gwamanatin Buhari na mika mulki ga shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya yi nisa.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana haka a wani martani kan batun da ke yawo a kafafen sadarwa cewa Buhari ba shi da niyyar mika mulki ga Tinubu.
Shehu ya kara da cewa Buhari ya kosa ya bar fadar shugaban kasa ya kuma koma mahaifarsa a Daura, da ke jihar Katsina.
Gidan Gwamnati, Abuja – Fadar shugaban kasa a ranar Juma’a, 24 ga watan Maris, ta karyata rahotannin da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da niyyar mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a karshen wa’adin mulkinsa ranar 29 ga watan Mayu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ya ce, tuni shirin gwamnati na mika mulki ya yi nisa, a cewar rahoton gidan talabijin na Channels.
Wani bangaren sanarwar ya ce:
”Fadar shugaban kasa na son sanar da cewa labarin karya ne kuma mara makama, ta kuma yi Allah wadai da jingina kalaman karya ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma yada shi.
‘Ta ya zaka tallata wani iya karfinka, ka zabe shi sannan ace ba za ka mika ma sa mulku ba? Wannan tunanin marasa ilimi ne.”
Read Also:
Shehu bayyana kafar yada labaran da ta wallafa rahoton (ba Legit.ng ba) a matsayin ”mara sanin ya kamata” ya kara da cewa mammalakinta ”ya dauki bangare a siyasa, hasalima ya fadi a zaben shugaban kasa.”
Daga Buhari zuwa Tinubu: Fadar Shugaban kasa ta yi bayanin shirin mika mulki
Shehu kuma cigaba da cewa a kafa kwamitin mika mulki, da ya hadar da wakilan gwamnatin Buhari da kuma gwamnati mai jiran gado ta Tinubu.
A cewarsa, kwamitin na tattaunawa kullum.
”Tuni gwamnati ta fara shirin mika mulki. Kwamitin mika mulki, da ya hadar da wakilan gwamnati mai barin gado da mai jiran gado su na tattaunawa kusan kullum don shirya yadda za a mika mulki ga gwamnatin Tinubu/Shettima,” in ji shi.
”Akwai kananan kwamitoci 13 da aka fitar daga babban kwamitin, wasu, don shirya faretin sojoji da kuma raka shugaba Buhari, sun fara aikinsu ko su na daf da farawa. Zuwa yanzu, komai na tafiya dai dai kuma ba alamun tangarda.”
Buhari ya matsu ya koma Daura, in ji Shehu
Shehu ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya kosa ya koma garinsu Daura, da ke Jihar Katsina, don more hutun barinsa aiki.
Ya ce al’ummar Daura sun fara shirye shiryen tarbar dan su bayan ”kammala mulkinsa cikin nasara har na wa’adi biyu tsahon shekara takwas.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 23 minutes 32 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 4 minutes 57 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com