Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi da cewa su dakata.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran sabon zaɓaɓɓen gwamnan Sunusi Bature Dawaki Tofa ya fitar, inda tace sabon gwamnan ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi na cikin gida da na waje da kada su amince da bai wa gwamnatin jihar bashi daga ranar 18 ga watan Maris zuwa ranar 29 ga watan Mayu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sabuwar gwamnatin ba za ta yi la’akari da bashin da jihar ta karɓa, ba tare da saninta ba daga ranar zaɓe zuwa ranar da aka rantsar da sabuwar gwamnatin.
Read Also:
Haka kuma sanarwar ta ce masu bin gwamnatin jihar bashi a yanzu su kwana da sanin cewa za a sake nazarin ƙa’idojin bashin bayan kammala bincike a kan kowanne bashi da ake bin jihar.
Ko a makon da ya gabata ma sabon zaɓaɓɓen gwamnan ya bayar da shawara ga masu gine-gine a filayen gwamantin jihar da su dakatar da ayyukansu.
To sai dai ‘yan kwanaki bayan shawarar zaɓaɓɓen gwamnan, gwamnan jihar mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje ya mayar masa da martani, yana mai cewa sabon gwamnan ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama’a.
duk da cewa ana kallon martanin na Gandujen ka iya zama musayar yawu tsakanin Gwamnatin mai ci da mai barin gado.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 4 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 45 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com