Jam’iyyar APC reshen jihar Kano da ke Najeriya ta shigar da kara a gaban kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamna, inda take kalubalantar Hukumar Zaben Kasar ta INEC kan yadda ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
Read Also:
Kazalika APC ta yi zargin cewa, NNPP ba ta lashe zaben ba musamman ganin yadda aka kidaya wa jam’iyyar hatta kuri’un da suka lalace a cewarta, kuma tana ganin cewa, da an cire lalatattun kuri’un, da ita za ta yi nasara.
Koda yake, dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna bai yi tarayya da jam’iyyar ba wajen shigar da wannan koken.
Tuni dai Gawuna ya amince da shan kayi a zaben wanda sakamakonsa ya nuna cewa, Abba Gida-Gida ya samu kuri’u miliyan 1 da dubu 19 da 602, yayin da shi kuma ya samu kuri’u dubu 890 da 705.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 6 hours 55 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 8 hours 37 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com