Gwamnatin Tarayya ta Bayar da Hutun Sallah
Gwamnatin Najeriya ta ayyana Juma’a 21 da Litinin 24 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutu don gudanar da shagulgulan bukukuwan ƙaramar sallah.
Ministan harkokin cikin gida na ƙasar Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana haka madadin gwamnatin tarayya.
Ministan ya kuma taya al’ummar musulman ƙasar murnar kammala azumin watan Ramadan.
Read Also:
Mista Aregbesola ya yi kira ga dukkan al’ummar musulmin ƙasar da su ci gba da ayyukan alkairin da suka koya a cikin watan na Ramadan.
Ya ce ”ina kira a gare ku da ku ci gaba da nuna wa juna halin dattaku, da soyayyar juna, da hakuri da juna da zaman lafiya da sadaukarwa da sauran kyawawan ayyuka, kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya koya mana”.
Ana sa ran gudanar da bikin ƙaramar sallah tsakanin ranar Juma’a da Asabar a Najeriya, yayin da ake daf da kammala azumin watan Ramadan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 19 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com