An shiga mako na biyu ana gwabza yaki a Sudan tsakanin sojojin kasar da kuma rundunar RSF, a daidai lokacin da wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimmawa yazo karshe.
Harbe-harbe da karar fashewar bama-bamai sun lafa sai dai an wayi garin Asabar da karar harbe-harbe, wanda hakan alama ce ta rugujewar yarjejeniyar da aka cimmawa ta tsagaita wuta.
Duka bangarorin biyu dai sun ta ikirarin cewa za su tsagaita wuta sai dai abin ya ci tura.
Read Also:
Fiye da mutane 400 ne suka mutu yayin da dubbai suka jikkata tun bayan da fada ya kaure ranar Asabar tsakanin rundunar soji karkashin jagorancin babban hafsan soji Abdel Fattah da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo da aka fi sani Hemeti, wanda ke shugabantar rundunar (RSF).
Ranar Juma’a rundunar sojin ta sanar cewa ta “amince ta tsagaita wuta ta kwana uku” domin “bai wa ‘yan kasar damar yin bikin karamar Sallah da kuma bari a kai kayan agaji”, kamar yadda Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken suka bukaci a yi.
Ganau a yankuna da dama na Khartoum sun ce an kwashe tsawon Juma’a ba tare da jin karar harbe-harbe da luguden wuta ba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 58 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 40 minutes 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com