Home SIYASA Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar jami’anta bisa hadarin...

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar jami’anta bisa hadarin mota

Wasu ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Ƴan sandan na tafiya ne zuwa karamar hukumar Giwa bayan halartar bikin Hawan Daushe a birnin Zariya a ranar Lahadi, inda hatsarin ya afku da misalin karfe 9 na dare.

An ruwaito cewa ɗaya daga cikin tayoyin motar ‘yan sanda ne ya fashe a kauyen Sako, a Kidanda, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar jami’an guda uku.

Wasu uku kuma sun jikkata, inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu a cewar majiyoyi.

Hotuna da aka gani, sun nuna jami’an jina-jina, inda wasu suka samu munanan raunuka a kawunansu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da yi wa jami’an da suka rasu addu’a da kuma fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp