Shafin twitter ya cire alamar Verification akan shafin tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osibanjo.
Kawo yanzu shafin na twitter bai bayyana dalilin daukar matakin ba.
Read Also:
Ita dai wannan Alama ta “Verification” na nuna inganci da tabbacin cewa wannan shafi na guda ne cikin Mahukunta a gwamnati domin gujewa sojan gona.
Wannan dai na zuwa ne bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar shi da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, suka mika ragamar kasar ga Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shatima.
PRNigeria hausa