Sabon gwamnan jihar Kano Injiniya, Abba Kabir Yusuf, ya fara daukar matakan binciken gwamnatin da ya gada ta Abdullahi Umar Ganduje, inda hawansa mulki ke da wuya ya bayar da umarni kan wasu tsauraran matakai.
Daga cikin matakan da ya fara dauka gwamnan ya soke dukkanin cinikin da aka yi na sayar da wasu wurare na gwamnatin jihar.
Tun dai a jawabinsa na bayan rantsuwa gwamnan ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro a jihar da su je su karbe iko da wadannan wurare da gwamnatin ganduje ta sayar.
Read Also:
Wasu daga cikin wuraren da aka sayar sun hada da filayen makarantu da na masallatai da makabarta da jikin badala da sauransu.
Matakin ba ya tsaya ga kadarorin gwamnati da ke cikin jihar ba ne har ma wadanda suke waje dokar soke cikin ta shafa.
Gwamnan wanda ya kuma sauke dukkanin shugabannin ma’aikatu da hukumomi da kamfanoni na gwamnati nadin siyasa har ma da hukumomin daraktoci na gudanarwa, da ma’aikatu da hukumomi da kamfanoni har da manyan makarantun jihar ya kara da cewa dukkanin matakan da zai dauka a kwanakin da ke tafe zai yi ne da nufin dawo da kima da martabar jihar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 42 minutes 8 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 23 minutes 33 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com