Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ne ya gayyaci su, shi da tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan rushe-rushen da ake yi a jihar.
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya ce Ganduje a matsayinsa na gwamna ya hana shi daga jihar Kano tsawon shekaru uku da rabi.
Read Also:
Da yake amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa, Kwankwaso ya yi ikirarin cewa yawancin gine-ginen da aka rushe gwamnatin Ganduje ce ta sayar da su, ba bisa ka’ida ba, kuma shugaban kasa Tinubu ya kadu a lokacin da ya yi masa bayanin hakikanin abin da yasa ake rushe gine-ginen a halin yanzu.
Da aka tambaye shi ko ya gamsu da sanya bakin da shugaban kasa yayi akan rushe gine-ginen, sai ya ce: “Shugaban ya kadu Shin ba za ku yi mamakin ace muku wani ya sayar da Jami’a ba? Baku yi mamakin yadda ya rusa jami’a ba? Wato Daula Hotel, ga wadanda suka San Kano, ai kun san tsohur Daula, wadda aka rushe, to fa wata tsangaya ce a cikin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, shin abun bai baku mamaki ba?” Inji Kwankwaso
“Shugaban kasar ya yi mamaki. Saboda bai sani ba. Ai lokacin Sallar idi ya karato da zaka yi Sallah a filin da kayi takaicin yadda aka mayar da wurin Sallah kasuwa.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 8 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 49 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com