Hamɓararren shugaban Nijar ya roƙi Amurka da “duka ƙasashen duniya” da su taimaka “wajen mayar da ƙasar kan tsarin Mulkin damukradiyya” bayan juyin mulkin da aka yi a makon jiya.
Read Also:
Cikin wata maƙala da ya rubuta a jaridar Washington Post, Shugaba Mohamed Bazoum, ya ce ya rubuta maƙalar ce a matsayin wadda aka yi “garkuwa” da shi.
Rashin kwanciyar hankali na ƙara ta’azzara a ƙasar da ke yammacin Afrika tun bayan hambarar da shugaban.
A ranar Alhamis, shugaban da ya jagoranci juyin mulkin ya sanar da kiran jakadunsu gida daga ƙasashen Faransa da Amurka da Najeriya da kuma Togo.
PRNigeria hausa