Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ya gabata na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya ce matakin dakatar da ministar jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu, abin yabawa ne,ko da yake bai isa ba.
Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar ne a jiya Litinin kuma ya umarci hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kanta, bayan ya fuskanci kiraye-kirayen a ɗauki mataki a kanta saboda zarge-zargen tafka almundahana, ko da yake ta musanta zarge-zargen.
Ministar da aka dakatar ta dai fuskanci gagarumar suka ne bayan kwarmata wasu takardun kashe kuɗi daga ma’aikatarta, waɗanda suka nuna ta bayar da umarni ga babbar akanta ta biya naira miliyan 585 cikin wani asusun ajiyar wata, lamarin da ake zargin ya saɓa ƙa’idojin kashe kuɗi na gwamnati.
Read Also:
A cikin wata wasiƙa da wani mataimakinsa na musamman Phrank Shaibu ya fitar, jagoran adawar Najeriya ya ce abin takaici ne ganin yadda shirin da aka kafa don tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci amma kamar yadda ake zargi ya zama saniyar tatsa ga gwamnatocin jam’iyyar APC.
Ya ce, “Ko da yake Tinubu ya cancanci yabo saboda dakatar da Betta Edu, amma mun yi imani, yunƙurin ya zo a makare. Da farko, ba shi da wata alaƙa ta naɗa ta a matsayin minista ta irin wannan muhimmiyar ma’aikata. Sai dai Tinubu ya fifita siyasa a kan ƙwarewa, lamarin da ya janyo wannan abin kunya.
Atiku wanda ya yi kira a yi wa ma’aikatar garambawul, ya kuma yi zargin cewa ba Betta Edu kaɗai ba ce da hannu a wannan badaƙala.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 5 hours 59 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 7 hours 40 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com