• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home General Jan hankali ga ‘yan uwa ‘yan Kwankwasiyya
  • General

Jan hankali ga ‘yan uwa ‘yan Kwankwasiyya

By
Daga Nazeer A. Adam
-
February 11, 2024
Arewa Award

Bari na fara da tariya;

A lokacin da Allah ya karbi rayuwar Kakan mu, ma’ana mahaifin jagora Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, Mai girma Majidadin Kano Alh. Musa Saleh, a cikin wadanda mukayi mamakin halartarsu Miller road domin yiwa Jagora gaisuwa akwai Mai martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero da sauran yan uwansa, duk da a al’ada ba mu saba ganin Sarkin kano yana zuwa ta’aziyya ba, wanda a lokacin dukkan mu da mukewa bin tsarin kwankwasiyya mun ji dadin wannan karamcin, kuma haka ya sanyayawa ran mu, da yawan mu munyi posting domin nuna jin dadin mu. WANNAN KARAMCI NE.

Ranar da Mai girma gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf ya ziyarci fadar mai martaba sarkin kano a zagayen yakin neman zabe, kowa ya shaida irin Karamcin da Mai martaba Sarki ya nuna wa tawagar mu, wanda a wannan lokacin ma mun cika duniya muna fadin tarbar mutunci da mai martaba Sarki yai mana. ANAN MA AN MANA KARAMCI.

Me ya biyo baya?

Ranar da aka yi bikin rantsuwar mai girma gwamna a filin kwallon kafa na kofar mata, Mai martaba Sarkin kano Alh. Aminu Ado Bayero da Dan uwansa Sarkin Bichi Alh. Nasir Ado Bayero sun halarci taron rantsuwa, wanda a nan filin taro aka samu wasu suna jifa da ihu da nuna rashin da’a a garesu, wanda duniya ta ga yadda Jagora ya nuna fushinsa a wajen, wadda har sai da ta kai ga Jagora ya rako Sarki zuwa mota domin nuna baya tare da wannan rashin albarkar da wasu suka aikata, Amma su waye suka aikata haka ?? Ku biyo ni a gaba.

Read Also:

  • Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi
  • Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15
  • Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi

Ranar da Mai girma gwamna zai sake bude asibitin Hasiya Bayero wanda aka kwato daga hannun wasu marasa kishi, anan ma mai martaba Sarkin kano Alh.Aminu Ado Bayero ya halarci bikin bude asibitin, amma anan ma aka sake samun wasu suka aikata rashin da’a ta hanyar yiwa Sarki Ihu da kunna wakokin da zasu bakantawa Sarki. Wanda anan kowa yaga yadda Mai girma gwamna Alh. Abba kabir Yusuf ya leko ta saman mota yana nuna fushinsa ga matasan da suka aikata wannan rashin da’ar. Wanda daga baya hukumar yan sanda ya gabatar da bincike akan wannan marasa tarbiyyar, inda aka a cikin wadanda aka kama, an wallafa vedionsu a shafin mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar kano, kuma anan duniya ta shaida cewa wasu yara ne, masoyan Mai girma tsohon Sarkin kano Muhammadu Sunusi ne suke shiga rigar mu ta kwankwasiyya domin aikatawa sarkin kano Aminu rashin da’a.

A abubuwan nan da na jero guda hudu, ta bayyana a fili cewa Da Jagora da Mai girma gwamna basa goyon bayan yadda ake shiga rigar mu ta kwankwasiyya domin cimma wata manufa.

Tunda anyi walkiya, mun ga kowa, To WALLAHIL AZEEM lokacin da wasu marasa mutunci zasu cigaba da shiga rigar mu ta kwankwasiyya su aikata rashin da’a ya wuce, Ba zamu zuba ido ba, Mun dai na bari

Na san da yawa zasuyi mamakin fitowar kalaman nan daga bakina ko ??

To bari na sake jaddada muku, NI DAN KWANKWASIYYA NE CIKAKKE.

Idan kuma akwai wanda zai min gorin bawa kwankwasiyya gudunmawa, to Bismillah.

Sai kun jini a Karo na biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • Abba gida-gida
  • kwankwasiyya
  • Kwankwaso
Previous articleKaso 30 na mace-macen Jarirai a Duniya na faruwa ne a Najeriya’
Next articleYadda ma’aikatan jinya da ungozoma suka gudanar da zanga-zanga a Abuja
Daga Nazeer A. Adam

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15

Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi

Hukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya

‘Yan sandan Jigawa sun kama Dilolin kwaya a jihar

Kofa ya sanar da ficewarsa da ga NNPP

Gwamnatin Najeriya ta yi maraba da ɗaure Simon Ekpa a Finland

Atiku ya nemi a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Rivers

An yanke wa ɗan Najeriya Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara 6 a Finland

Sojoji da DSS sun kashe ƴan bindiga 50 a jihar Neja

ASUU na barazanar shiga yajin aiki a jami’o’in Najeriya

Gwamnan jihar kebbi ya amince da naɗin sabon sarkin Zuru

Recent Posts

  • Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi
  • Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15
  • Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi
  • Hukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru
  • NUPENG ta cimma matsaya da kamfanin Dangote

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1550 days 14 hours 48 minutes 37 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1532 days 16 hours 30 minutes 2 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗiKotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin MauludiHukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar AnsaruNUPENG ta cimma matsaya da kamfanin DangoteƘungiyar ƙwadago ta TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki a NajeriyaEl-Rufa'i ya shigar da ƙorafi kan zargin ƴansanda da cin zarafi'Yan sandan Jigawa sun kama Dilolin kwaya a jiharKofa ya sanar da ficewarsa da ga NNPPBurkina Faso ta amince da dokar haramta neman maza a faɗin ƙasarAn bayyana jihohin arewacin Najeriya da za su iya fuskantar ambaliya a watan SatumbaGwamnatin Najeriya ta yi maraba da ɗaure Simon Ekpa a FinlandAtiku ya nemi a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin RiversAn yanke wa ɗan Najeriya Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara 6 a FinlandSojoji da DSS sun kashe ƴan bindiga 50 a jihar Neja
X whatsapp