Ana cigaba da zaman makoki na kwanaki uku a ƙasar Kenya don jimamin mutuwar babban hafsan hafsoshin tsaron kasar (CDF) Janar Francis Omondi Ogolla wanda ya mutu a wani jirgin sama da ya yi hatsari a lardin Elgeyo Marakwet da ke arewa maso yammacin kasar.
Ogolla, mai shekaru 61, ya mutu ne ranar Alhamis tare da wasu jami’an soji 9 da suka yi masa rakiya zuwa wani aiki na tantance yanayin tsaro a yankunan arewa maso yammacin Kenya da ke fama da matsalar rashin tsaro.
Read Also:
A wani jawabi da ya yi wa al’ummar kasar sa’o’i bayan hatsarin jirgin, shugaba William Ruto ya ce Kenya ta yi asarar “ɗaya daga cikin manyan hafsoshinta”.
Tsohon shugaban ƙasar Uhuru Kenyatta da jagoran ‘yan adawa Raila Odinga da jakadiyar Amurka Meg Whitman na daga cikin jagororin da suka yi ta’aziyyar mutuwar babban jami’in sojin na Kenya.
Marigayi Janar ɗin ya shiga rundunar sojojin Kenya (KDF) a shekara ta 1984 kuma ya kai matsayin babban kwamandan sojojin ƙasar a bara.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1241 days 14 hours 11 minutes 20 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1223 days 15 hours 52 minutes 45 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com