An kama gwamman masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a jami’o’in Amurka, yayin da tashin hankalin ɗalibai ke ƙaruwa a jami’o’in.
Lamarin ya fi ƙamari a Jamiar Texas, inda ‘yan sanda a kan dawaki suka hana masu zanga-zangar kafa sansani, sai kuma wadda aka yi a California.
Read Also:
Wasu na ɗora alhakin a kan masu tsattsauran ra’ayi daga wajen jami’o’in, waɗanda suka yi nasarar kutsawa haraba makarantun.
Wasu daga cikin jami’an gwamnati na kira da a ɗauki tsattsauran mataki a kan masu zanga-zangar, da cewa masu aƙidar ƙyamar Yahudawa ne.
PRNigeria Hausa