Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Xavi ya amince ya cigaba da jagorantar kungiyar bayan ya sami karfin gwiwa daga mamallaka kungiyar da manajojinta da duk masu ruwa da tsaki.
“Ni kaina, abokan aikina, dukan mu muna jin cewa muna da ƙarfin da zamu cimma abu mai muhimmanci tare kuma mu cigaba da yin wannan aikin tare.”
Read Also:
Kungiyar kwallon kafa ta Bercelona dai na fuskantar koma tasgaro a baya bayan na, tun bayan da aka cire ta daga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, sa’annan kungiyar kwallon kafa ta real Madrid dake matsayin babbar abokiyar hamayyarta a kasar Spain ta lallasata a ci 3 da 2 a wasan Elclassico.
a kwanakin baya ne dai mai horar da kungiyar Xavi wanda tsohon dan wasan kungiyar ne, ya ayyana kudirinsa na Ajje aikin horar da kungiyar, bisa kwamgaba-kwambaya da take samu a karkashin kulawarsa.
Duk da cewa dai kungiyar ta Bacerlona ita ce ta lashe gasar ta laliga a kakar bara, to yanzo dai tana matsayi na biyu a bayan Madrid.
kungiyar ta Real Madrid dai na saman teburi da maki 81 a cikin wassani 32, wadda Barcelonan ke biye mata da maki 70 a gasar ta laliga.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 32 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 13 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com