Amurka za ta janye wasu daga cikin dakarunta daga Chadi na wani ɗan lokaci, kwanaki bayan da ta amince ta janye duka dakarunta daga Nijar mai maƙwabtaka.
Sakataren yaɗa labarai na ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon, Manjo Janar Pat Ryder ya ce Amurka za ta sakewa wasu daga cikin sojojin wuri daga Chadi amma bai ce suwa ne waɗanda matakin zai shafa ba ko kuma inda za a kai su.
“Wannan mataki ne na wucen gadi a yunƙurin sake nazari kan haɗin gwiwar tsaro da za a ci gaba da yinta bayan zaɓen shugaban ƙasar Chadi na ranar 6 ga watan Mayu.” kamar yadda ya bayyana.
Read Also:
Sanarwar ta zo ne bayan da shugaban hafsan sojin saman Chadi, a farkon watan nan, ya umarci Amurka ta dakatar da ayyukanta a sansanin sojin sama da ke N’Djamena, babban birnin Chadi, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Gen Ryder ya kuma ce an soma tattaunawa da sojojin da ke mulki a Nijar da majalisar tabbatar da tsaron ƙasa CNSP ranar Laraba domin tabbatar da janye sojojin Amurka daga ƙasar cikin lumana.
Amurka ta dogara kan Nijar a matsayin babbar sansaninta ta bibiyar ayyukan ƴan ta’adda a yankin Sahel.
Sai dai sojojin Nijar da ke mulkin ƙasar tun Yuli, sun kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro da ƙasar tare da korar sojojin Faransa, wani yunƙuri na yanke alaƙa da ƙasashen yamma.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 26 minutes 19 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 7 minutes 44 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com