Gwamna Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashin N70,000 ga ma’aikatan Edo

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan gwamnati daga N30,000 zuwa N70,000 a jihar.

Gwamna Obaseki ya bayyana hakan ranar Litinin lokacin da yake ƙaddamar da ginin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar.

A cewar gwamnan, sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu.

Matakin gwamnan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙwadagon ke matsa wa gwamnatin tarayya lamba don ta ƙara mafi ƙarancin albashin domin rage wa ma’aikata raɗaɗin hauhawar farashi.

NLC da TUC sun nemi gwamnati ta mayar da mafi ƙanƙantar albashin ya zama N615,000.

Tun a watan Janairu ne gwamnatin Bola Tinubu ta kafa kwamitin mutum 37 da ke da wakilci daga ɓangarori da dama – gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyar ƙwadago.

Kwamitin zai tattauna domin tsayar da mafi ƙarancin albashin da zai gabatar wa gwamnati domin amincewarta.

A lokacin ƙaddamar da kwamitin, mataimakin shugaban ƙasa, Kassim Shettima ya nemi kwamitin ya gaggauta wajen cimma matsaya, ya kuma miƙa rahotonsa da wuri.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 27 minutes 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 9 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com