Kotu nada hurumin saurarar karar Dambarwar Masarautar Kano – Kotu

Babbar Kotun tarayya dake Jihar Kano a Arewacin Najeriya, ta ce tana da hurumin sauraron ƙarar da Alhaji Aminu Babba Ɗan agundi ya shigar akan batun dambarwar Masarautar Kano.
Kotun ƙarƙashin Jagorancin mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman tayi ƙwarya-ƙwaryar Hukuncin ne, biyo bayan inkarin da ɓangaren waɗanda ake ƙara suka yi na cewar kotun bata da hurumin sauraron ƙarar.
A zaman baya dai an tafka muhawara a tsakanin ɓangarorin biyu wato ɓangaren masu ƙara da waɗanda ake ƙara akan batun hurumin kotun dangane da Shari’ar, harma kotun ta ayyana yau Alhamis a matsayin ranar da zata bayyana matsayar ta akan batun hurumin.
Kuma tuni kotun ta ɗage zaman Shari’ar zuwa ranar 26 ga watan nan na Yuni domin ci-gaba da sauraron shariar bayan ta tabbatar cewa tana da hurumin sauraron ƙarar.
Ɓangaren Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ne dai suka shigar da ƙarar, a sakamakon rashin amince wa da matakin Gwamnatin Kano na rushe Masarautun jihar guda biyar bayan da Majalisar dokokin jihar tayi wa dokar Masarautun Garambawul.
PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 56 minutes 58 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 38 minutes 23 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com