Biden ya janye daga takarar Shugabancin kasar Amurka

Shugaban kasar Amurka Joe biden ya dakatar da yakin neman zabensa a ranar lahadi.

wannan ya biyo bayan hukuncin da jam’iyyar sa ta demukrat ta yanke kan ingancin lafiyar kwakwalwarsa, da kuma binda take gani matsami nakasu a takarar tasa da Donald Trump.

Biden ya wallafa a shafin sa X cewa zai kasance a mukamin sa na shugaban kasar Amurka kuma shugaban rundunar sojojin kasar har zuwa lokacin da wa’adin mulkin sa zai kare a watan janairun 2025.

Haka kuma yace zai yiwa Al’ummar kasar jawabi a cikin wannan makon mai kamawa.

An dai ta kai ruwa rana kafin shugaban kasar kuma dan takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam’iyyar Demukrat ya janye daga takarar bisa zargin tsufa da kuma rashin ingantacciyar lafiyar kwakwalwa.

”A lokacin da muka ɗauka muna mulki mun samar da muhimman abubuwa ciki har da dokar mallakr bindiga”.

Shugaban ya kuma goyi bayan mataimakiyar Kamala Haris a matsayin wadda za ta yi takarar shugabancin ƙasar a madadinsa.

”A yau ina son in jaddada cikakken goyon bayana ga Kamala a matsayin ‘yar takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyarmu, lokaci ya yi da za mu haɗa kai wuri guda domin kayar da Donald Trump”, kamar ya wallafa a shafinsa na X.

A makon da ya gabata ne gwaji ya tabbatar da cewa shugaban ya kamu cutar korona, inda ya killace kansa a gidansa da ke Delaware, to sai dai a ranar Juma’a ya ce ya samu sauƙi, kuma zai ci gaba da yaƙin neman zaɓen sa cikin makon mai zuwa.

A baya dai shugaban ya ce ”Allah ne kawai” zai hana shi tsayawa takara bayan da aka yi matsa masa lamba kan ya haƙura da takarar, to sai dai daga baya ya ce zai iya haƙura da takarar bisa sharaɗin lafiya..

A baya-bayan nan dai shugaban ya fuskanci matsin lamba daga manyan ‘yan jam’iyyarsa da ke kiraye-kirayen ya haƙura da takara, tun bayan rashin katabus a muhawarsa da Donald Trump.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 36 minutes 47 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 18 minutes 12 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com