Kwamitin yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce an yi masa kutse a cikin bayanansa na cikin gida, kuma ya nuna alamun jami’an Iran ne ke yin hakan.
Shafin jaridar intanet ta Politico da ke Amurka, a jiya Asabar ya bayar da rahoton cewa an aika masa wasu takardun yaƙin neman zaɓe ciki har da takardun bincike na cikin gida da kwamitin yaƙin neman zaɓen na Trump ya yi a kan mataimakin Trump ɗin a zaɓen da za a yi, Sanatan Ohio, JD Vance.
Wani mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ya gaya wa BBC cewa :“An samu waɗannan takardu ne ta haramtacciyar hanya daga wasu kafofi na ƙasar waje, da ke gaba da Amurka, da nufin katsa-landan a zaɓen 2024.”
Jaridar Politico ta ce ta tabbatar da sahihancin takardun, ko da yake wasu jaridu na duniya basu tabbatar da sahihancin ba.
Sai dai kwamitin yaƙin neman zaɓen bai bayar da cikakken bayani ko wata sheda da ke tabbatar da takardun da aka yi satar fitar da su ba ga masu kutse na Iran ko kuma gwamnatin Iran.
Ko a lokacin zaɓen shugaban Amurka na 2020 kamfanin Microsoft ya fitar da irin wannan rahoton, da cewa masu kutse na Iran na harin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa.
Kamfanin ya ma ƙara da cewa masu kutsen na Iran sun yi haka a kai-a kai aƙalla a zaɓe uku na shugaban ƙasa a Amurka.
Haka su ma jami’an tsaron Amurka sun yi gargaɗin cewa Iran na shirin hallaka Donald Trump, to amma wannan ba shi da alaka da harin da aka kai masa a watan da ya wuce a Pennsylvania.
Kuma a ranar Talata ma’aikatar shari’a ta Amurka ta tuhumi wani ɗan Pakistan da ake zargi yana da alaƙa da Iran da shirin kashe jami’an Amurka, wanda a iya cewa har ma da shugaban ƙasar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 39 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 21 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com