Gwamnatin Nijeriya ta amince a kori ma’aikata masu takardar karatu ta bogi daga ƙasar Benin da Togo

Gwamnatin Najeriya ta bayar da amince a kori duk ma’aikata na gwamnati da waɗanda ba na gwamnati ba, waɗanda suke da takardar shedar karatu ta bogi, da suka samu daga Jamhuriyar Benin da Togo,

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman shi ne ya bayyana haka a, yayin wani taron manema labarai, jiya Juma’a a Abuja, lokacin da yake bayyana irin nasarorin da ya ce ya samu a tsawon shekara ɗaya a ma’aikata.

Mamman ya ce an amince da matakin ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta ƙasar kwanan nan.

Ministan ya bayyana cewa ƴan ƙasar sama da 22,500 ne ke ɗauke da takardar shedar karatu ta bogi da suka samu daga ƙasashe irin su, Jamhuriyar Benin da Togo, a tsakanin 2019 da 2023.

Ya ce sama da ɗalibai 21, 600, suka samu takardun shedar karatun daga jami’o’in da ba a tabbatar da ingancinsu ba a Jamhuriyar Benin yayin da 1,105 su ma suka samu irin waɗannan takardu daga jami’o’in da ba a tabbatar da ingancin nasu ba a Togo.

Ya ƙara da cewa a don haka ne gwamnati ta kafa wani kwamiti na musamman na haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatu domin gudanar da bincike kan takardun shedae karatun, cibiyoyin da ke wannan cuwa-cuwa a ciki da wajen Najeriya.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 5 hours 49 minutes 13 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 7 hours 30 minutes 38 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com