Gwamnatin Najeriya ta bakin Hukumar Ruwa ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency (NIHSA) ta ce za ta gina wasu madatsun ruwa biyar domin kare ambaliyar da ke faruwa a sanadiyar ruwan da ke mamal daga dam ɗin Lagbo na Kamaru.
Darakta-Janar na NIHSA, Umar Mohammed ne ya bayyana hakan a zantawarsa ta talabijin na Channels a ranar Alhamis.
Hukumar ta gargaɗi ƴan Najeriya da suke zaune a wuraren da ake ambaliya su canja mazauni saboda sako ruwan da aka yi daga Kamaru.
Jihohin da ake fargabar dam ɗin na Kamaru zai jawo ambaliya sun haɗa da Adamawa da Taraba da Benue da Nasarawa da Kogi da Edo da Delta da Anambra da Bayelsa da Kuros Riba da Rivers.
Mohammed, wanda daraktan aikace-aikace na hukumar Femi Bejide ya wakilta, ya ce hukumar ta miƙa wa Fadar Shugaban Ƙasa rahoto, inda a ciki ta bayyana hanyoyin da za a kiyaye aukuwar ambaliyar, ciki har da sauya wuraren da wasu dam suke.
“Sannan mun miƙa buƙatar gina wasu dam guda biyar domin tare ruwan dam ɗin Lagdo,” in ji shi.
“Amma dole za a canja inda wasu dam suke, sannan a faɗaɗa gaɓar tekunan Neja da Benuwe.”
Sako ruwan dam ɗin Lagdo ya zo ne kwanaki kaɗan bayan dam ɗin Alau a Maiduguri ya yi ambaliya, inda aƙalla mutum 30 suka mutu, sannan ya raba dubbai da muhallansu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 39 minutes 58 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 21 minutes 23 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com