Wani harin mayaƙa masu iƙirarin jihadi da aka kai sansanin horar da sojoji da filin tashi da saukar jiragen sama na babba birnin Mali, Bamako ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 70 tare da jikkata 200, adadi mafi muni na jami’an tsaro da aka taɓa samu a shekarun baya-bayann nan.
Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa mutanee 77 ne suka mutu, kana 255 suka samu raunuka a harin da aka kai Bamako a ranar Talata.
Zalika, wani bayanin sirri na hukuma da aka tantance sahihancinsa ya ce adadin waɗanda suka mutu ya kai kimanin ɗari, inda ya bayyana sunayen 81 daga cikin su.
Read Also:
Jaridar Le Soir da ake wallafawa a kasar ta ranar Alhamis ɗin nan ya ruwaito cewa a ranar aka yi jana’izar kimanin dakaru masu karɓar soji kimanin 50.
Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto mahukuntann gwamnatin sojin Mali ba su fitar da ainihin adadin waɗanda su ka mutu a harin da ƙungiyar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai wa ba.
Ƙwararru sun ce harin sshi ne naa farko irin sa a cikin shekaru, kuma ta yi mummmunan tasiri a kan gwamnatin sojin ƙasar.
Ba a cika samun hare-hare a babban birnin ƙasar Mali kamar yadda ake samu a sauran sassan ƙasar kusan kullayaumin ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 12 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 53 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com