Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta EFCC ta tsare tsohon Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku bisa zargin halasta kudin haram ya zuka kai naira biliyan 27 a lokacin da yake bisa karagar mulkin jihar
EFCC ta na tuhuwar tsohon Gwamnan wasu tuhume-tuhume guda goma sha biyar dake da nasaba da almundahana da dukiyar al’umma
Read Also:
Rahotanni sun bayyana cewa, a wannan Juma’a ne jami’an EFCC suka yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan da ke Abuja wanda wa’adinsa ya ƙare a shekarar 2023 bayan shafe tsawon shekaru takwas a kan madafun iko.
EFCC ta ce gwamnan yana hannun hukumar inda ake titsiye shi.
Hukumar ta EFCC ta kammala tattara aƙalla tuhume-tuhume 15 da ake zargin tsohon gwamnan kuma nan ba da jimawa ba zai gurfana a gaban kuliya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 24 minutes 33 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 5 minutes 58 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com