Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero, ya ce sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar ƴan Lakurawa, inda suka tsallaka zuwa Nijar.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Aliero ya ce an samu nasarar ne bayan ɗaukar matakin da ministan tsaro Abubakar Bagudu da babban hafsan tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka ɗauka, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
Aliero ya ce, “mun faɗa wa ministan cewa idan aka yi sakaci da ƴan ta’addan Lakurawa, za a iya maimaita abin da ya faru a arewa maso gabas a arewa maso yamma. Yaƙi ne da za a iya gamawa a kwana biyar, amma idan aka yi sakaci, lamarin zai ƙazance saboda yankin arewa maso yamma ya fi yawan mutane kuma ya fi arziki da ma girman ƙasar noma da kiwo.
“Amma kun san da sojoji suka zo a ranar Talata (12 ga Nuwamba) sun samu nasarar fatattakarsu zuwa Jamhuriyar Nijar?”
Ƴan Lakurawa sun kashe mutane da dama a jihar Kebbi, lamarin da ya sa Sanata Aliero da sauran ƴan majalisar jihar suka kai ziyara a ƙananan hukumomin Argungu da Augie domin gane wa idonsu irin ɓarnar da suke yi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 33 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 15 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com