• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home General An saka ranar gudanar da gasar CHAN ta Afirka
  • General
  • WASANNI

An saka ranar gudanar da gasar CHAN ta Afirka

By
Bakoji
-
January 29, 2025
Arewa Award

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta tabbatar da ranar da za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka (CHAN) na shekarar 2024 da aka ɗage a baya.

Hukumar kwallon kafar Afirka ta bayyana cewa a yanzu za a gudanar da gasar ta CHAN daga ranar 2 ga watan Agusta zuwa 30 ga watan Agustan 2025.

Tun a watan Fabrairun 2025 ne aka shirya gudanar da gasar karo na takwas, wanda kasashen Kenya, Tanzania da Uganda za su dauki nauyin shirya gasar, amma an dage gasar saboda kalubalen samar da ababen more rayuwa da ingantattun wurare.

An tabbatar da sabuwar ranar da za a gudanar da gasar ne a yayin taron kwamitin zartarwa na CAF da aka gudanar a ranar Litinin a birnin Rabat na kasar Morocco, karkashin jagorancin shugaban CAF Dr. Patrice Motsepe.

Read Also:

  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai
  • Gwamnonin PDP na taro a Zamfara
  • Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

Gasar ta CHAN ta keɓenta ne ga ‘yan wasan da ke taka leda a gasannin cikin gida, kuma Senegal ce ke rike da kambun gasar, bayan da ta lashe gasar karshe da aka yi a Algeria.

Kwamitin zartarwa na CAF ya kuma yanke shawara kan wasu gasanni masu zuwa, da kuma fara gasar cin kofin Afrika ta mata ta da za a yi a Morocco daga 22-30 ga Afrilu 2025.

Wadanda su ka kai wasan karshe a gasar za su samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta (FIFA Futsal) da za a yi a Philippines a cikin shekara.

An kuma amince da wani sabon tsari na neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika na U-17 na shekarar 2025, inda adadin kasashen da ke halartar gasar ya karu daga 12 zuwa 16.

Kwamitin zartaswa ya kuma amince da fara tsarin bayar da damar karbar bakuncin gasa a nan gaba, ciki har da gasar zakarun Turai ta mata (2005, 2026 & 2027), U-17 AFCON (2026, 2027 & 2028), da U-20 AFCON (2027, 2029 & 2031).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Previous articleECOWAS ta tabbatar da ficewar Nijar, Burkina Faso da kuma Mali a hukumance
Next articleGwamnatin Nijeriya ta dakatar da Jirgi Max Air
Bakoji

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Gwamnonin PDP na taro a Zamfara

Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

kotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele Kyari

Ana neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a Sokoto

A biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati – ASUU

EFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsare

Atiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yi

PDP ta zargi APC da yunkurin kawo tasgaro a Damukradiyya

Hoton Tinubu

Fadar Shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗin rashin lafiyar Tinubu

Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje da dama a Filato

Gwamnati ta yi hasashen samun ambaliya a jihohin Najeriya 19

Gwamnan Kano ya amince da murabus din Kwamishinan Sufuri Ibrahim Ali Namadi

Recent Posts

  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai
  • Gwamnonin PDP na taro a Zamfara
  • Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa
  • Hukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kano
  • kotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele Kyari

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1529 days 4 hours 3 minutes 40 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1511 days 5 hours 45 minutes 5 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kaiGwamnonin PDP na taro a ZamfaraYa kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai - MusaHukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kanokotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele KyariAna neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a SokotoA biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUUAmurka za ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyiEFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsareMajalisar Dokokin Kano ta Dakatar da Ciyaman din RanoƘananan dillalan mai sun zargi shugabanninsu da yiwa Matatar Dangote zagon ƙasaAtiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yiPDP ta zargi APC da yunkurin kawo tasgaro a DamukradiyyaFadar Shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗin rashin lafiyar Tinubu
X whatsapp