Bincike: Shin da gaske ne Tinubu ya nemi Faransa ta girke sojojinta a Nijeriya domin yakar Boko haram?

IKIRARI:

Wani ikirari da shahararren mai amfani da kafafen sada zumunta na zamani, Mahdi Shehu ya wallafa a shafinsa X da aka fi sani da Twitter ya bayyana cewa faransa na shirin kafa sansanin sojojinta a Nijeriya.

Shehu ta cikin wallafar ya kuma da hada da faifan bidiyo dake nuna wani babban jami’in sojojin Nijeriya, a kusa da shi kuma akwai wani Jami’an sojin waje, wanda ya yi wukar kugu da bidiyon matsayin hujja.

Wallafar ta Mahdi Shehu, wadda ta samu karbuwa a manhajar, domin kuwa mutane dubu 2 sun sake wallafata, yayin da mutane dubu dari 3 suka gani, dake bayyana yadda Gwamnatin Faransa ke shirin girke sojojinta bisa yunkurin tallafawa sojojin Nijeriya wajen yakar kungiyar Boko Haram, duk kuwa da musanta zargi da mahukuntan suka yi.

Ya nanata cewa samar da wannan alaka zai sa a samar sansanin sojojin a wuraren da ke fama da matsalar tsaro kama daga Maiduguri, Sokoto, Zamfara da Kogi domin magance matsalar, wanda kuma a fakaice za’ayi amfani da damar wajen hakar ma’adanai. Shehu yace hakan zai taimaka wajen dankwafe karfin iko da Nijeriya ke da shi matsayinta na kasa mai cin gashin kanta, zai sa ta zama tamkar wata kasa dake cikin mulkin mallaka karkashin Faransa, wanda kuma Bola Tinubu ne ya shirya hakan domin tabbata kan mulki.

Ya kuma kalubalanci jami’an sojojin Nijeriya kan amincewa da wannan yunkuri, wanda yace sun ci amana aikin su, matsayin su na wadanda ke da alhakin lura da tsaron kasa.

Tantancewa:

Domin tantance sahihancin ikirarin, PRNigeria ta gudanar bincike ta hanyar amfani da manhajar gane hoto, inda ta saka hoton farar fatar dake kusa da sojojin Nijeriya, wanda Mahdi ya yayi ikirarin sojan Faransa ne, wanda kuma yayi amfani da shi matsayin hujjar sojojin faransa sun kafa sansani a Nijeriya.

Bincike ya gano cewa sojan kasar wajen ba wani bane face Kanal Martin Leach, wanda sananne ne a cikin tawagar dakarun sojojin Birtaniya na (BMATT). Ya rike mukamin shugaban tawagar ta BMATT, wanda kuma yana bayyana yadda hadin gwiwa zai kasance tsakanin sojojin birtaniya da hukumomin Nijeriya

Wannan dalilin ya sa, PRNigeria ta sake sanya wasu harrufa dake da alaka da ikirarin a kafar internet a da sunan, wanda kuma ya bayyana rahotannin da dama a cikin labaran Nijeriya da wasu shafukan da dama. Misali a watan Maris na shekarar 2024, Colonel Leach ya jagoranci wakilnci daga sashin bada shawara na rundunar sojin Birtaniya (BMATT) wata ziyarar ta musamman zuwa kwalejin horas da sojijon ta NDA, wanda suka sami tarba daga Kwamandan Kwalejin Manjo Janar JO Ochai, wanda suka tattauna al’amura da dama ciki harda batun hadin gwiwa tsakanin NDA da BMATT.

Haka kuma, a wata Agustan 2024, Leach ya jagoranci tawagar BMATT domin bayar da wani horo na musamman ga dakarun sojoji don maganci ayyukan su, ga sojojin kasan Nijeriya a kwalejin horas da soji rukuni na 81 (DTS) a Owode dake jihar Ogun. An shirya horon ne domin dakile matsalar rashin tsaro.

Da yake jawabi a yayin bikin kaddamarwar, Shugaban rundunonin sojin Nijeriya Marigayi Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda ya sami wakilcin shugaban sashin horo (sojoji), Manjo Janar Sani Mohammad, ya yaba da hadin gwiwar tsakanin dakarun sojin Njieriyar da BMATT. Ya ce hada gwiwar gwiwar horaswa da hanyoyin gane abubuwa masu fashewa (IED), dakaru na musamman ya haifar da sakamako mai kyau.

A watan oktoban 2024, rundunar sojojin Nijeriya, ta hannun Kanal Martin Leach ta rabauta da kayayyakin yaki da kudinsu ya haura naira biliyan daya (£450,000) daga daga Birtaniya, domin kara karfi ga ayyukan yakar masu tsatstsauran ra’ayi a yankin arewa maso gabashin kasar.

Yayin damka kayan yakin ga mahukuntan kasar a garin maduguri, an mika su hannun kwamandan rundunar hadin gwiwa ta (JTF NE) Manjo Janar Wahidi Sha’aibu.

Ko da yake dakarun tsaro na rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) sun musanta labarin dake yawo a kafafen sada zumunta na cewa faransa na shirin kafa sansanini sojojinta a garin na Maiduguri, a jihar Borno.

Ta cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na dakarun Captain Reuben Kovangiya ya fitar, sun musanta ikirari, wand aya ce babu wani shiri na aiwatar da hakan ko yunkurin yin hakan.

Sanarwar ta ce Bidiyon da shehu ya saka matsayin hujja, wanda ya nuna Birgediya Janar Haruna na ganawa da mai shawarci na musamman a shashin horo na rundunar sojojin birtaniya (BMATT), ba sojan wakilin sojojin Faransa bane. Wannan abun ya faru ne lkacin da OPHK ta rabauta da tallafin kayan aiki da ga BMATT a ranar 25 ga watan oktoban 2024, a garin Maimalari dake birnin Maiduguri.

Rahotannin da dama sun tabbatar da cewa Kanal Martin Leach ya yi ziyara ta musamman a garin Maiduguri a cikin watan Oktoban 2024. Wakilan sashin bada shawara da horo na (BMATT) sun je Nijeriya ne domin su bayar da horan aikin soji da shawarwari da rudunar sojojin kasar. Dakarun suna Nijeriya ne domin yin aiki kafada da kafada da sojojin kasar domin habakawa gami da inganat ayyukan rundunar.

Da yake magana da PRNigeria kan lamarin, daraktan lura da bayanai na rundunar (DDI) birgediya Tukur Gusau ya tabbatar da cewa BMATT na aiki horar wa ne kawai ba yaki ba.

“Duba sosai za ka ga jami’an dake tambayar ya sanya kayan sojoji na Birtaniya, ba na faransa bane, amma sojojin birtaniya suke bamu horo kan makaman da suka samar mana,” a cewar sa.

A Takaice:

Binciken da PRNigeria ta yi ya nuna zargin da Mahdi shehu ya yi kan sojojin Nijeriya na samar da sansanin sojojin faransa a kasar, wanda yayi amfani da hoton Kanal Martin Leach, sojan birtaniya kuma sanne a cikin dakarun BMATT wanda ke matsyin kwamanda dakarun ba sojan faransa bane.

PRNigeria ta tabbatar da cewa labarin da Mahdi shehu ya wallafa a shafin sa na X (twitter) dake cewa faransa ta kafa sansanin sojojinta a arewacin Nijeriya labari ne na KARYA.

PRNigeria

 

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 18 hours 37 minutes 56 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 20 hours 19 minutes 22 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com