Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bawa Jami’ar Bayero umarnin dakatar da rushe -rushen da ta ke yi a garin Rimin Zakara.
Gwamnan ya bada umarnin ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya da kuma jajen abinda ya faru ga alummar yankin.
Read Also:
Abba Kabir ya kuma yiwa alummar alkawarin kawo karshen rikicin filayen da ke gudana tsakanin Jami’ar BUK da alummar Rimin Zakara wanda ya shafe sama da shekaru 30.
Dangane da wadanda suka rasa rayukansu gwamna Abba kabir ya bayar da umarnin kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin tare da daukar dawainiyar iyalansu.
Hakazalika Gwamnan ya ba da umarni samawa alummar yankin asibitin sha -ka-tafi tare da Gina musu masallacin juma’a.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf na bayar da umarnin daukar nauyin wadanda Suka Sami raunuka sakamakon abinda ya faru a yankin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 9 hours 58 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 11 hours 40 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com