Jam’iyyar APC ta saka ranar Talata 25 ga watan Fabrairu da Laraba, 26 ga Fabrairu domin gudanar da taron masu ruwa da tsaki, da kuma babban taronta.
Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajuddeen Bashiru ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.
Sanarwar ta ce za a yi taron masu ruwa da tsakin a daƙin taro na Banquet da fadar shugaban ƙasar Najeriya, sannan a gudanar da babban taron jam’iyyar a ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.