Gwamnonin PDP 11 sun shigar da ƙara don kalubalantar dakatar da Fubara

Wasu gwamnoni 11 karkashin jam’iyyar PDP, sun shigar da ƙara gaban kotun koli inda suke kalubalantar dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

Ƙarar da gwamnonin suka shigar ranar Talata, na kuma kalubalantar ayyana dokar ta-baci da aka yi a jihar.

Gwamnonin jihohi da suka shigar da ƙarar sun haɗa da Adamawa da Enugu da Osun da Oyo da Bauchi da Akwa Ibom da Plateau da Delta da Taraba da Zamfara da kuma Bayelsa.

A ƙarar da suka shigar, gwamnonin na kuma son kotun kolin ta ayyana cewa ko shugaban ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓen gwamna na jiha.

Sun kuma buƙaci kotun ta yanke hukuncin cewa ko yadda shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar ta Ribas bai saɓa wa kundin tsarin mulki na 1999 ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com