Rundunar sojin Mali ta bayyana cewa, wasu da ake zargi masu iƙirarin jihadi ne tare da haɗin gwiwar ‘yan tawayen FLA, sun ƙaddamar da wani mummunan hari akan wata tawagar sojojin ƙasar a ranar Litinin ɗinnan da ta gabata, a yankin arewacin ƙasar. Sai dai rundunar bata ba da cikakken bayani kan yadda lamarin ya kasance ba.
Read Also:
Bayanai sun nuna cewa bayan da maharan suka kammala aika-aikar tasu a Kidal da safiyar ranar Litinin ɗin, sai suka zarce yankin Anefis domin aiwatar da wata manufar tasu.
Sannan yan tawayen FLA suka bayyana cewa wannan harin sun iske motoci guda hudu a wurin, ciki har da mota mai sulke guda daya, a yayin da suka yi ikirarin cewa sun kwashesu tare da ikirarin cewa sun yi sanadin sanadin mutuwar mutane da dama.
Rundunar sojin Mali a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Litinin, ta ce an yi arangama, amma ba tare da ba da cikakken bayani kan taho mu gamar da suka yi ba.
Sai dai ‘yan tawayen na FLA sun ba da wata sanarwa akan harin da jirgi mara matuƙi ya kai musu a yankin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1490 days 7 hours 18 minutes 45 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1472 days 9 hours 10 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com