Sojojin Nijeriya sun hallaka mayakan boko haram 5 a jihohin Borno da Taraba

Dakarun sojin Nijeriya na ci gaba da samun nasarar a yakin da suke na kawar da matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin arewa maso gabashi da arewa ta tsakiyar Kasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da sojojin suka sami nasarar hallaka ‘yan ta’adda biyar a mabambanta hare-hare da suka kai a jihohin Borno da Taraba kamar yadda PRNigeria ta sami bayani.

A jihar Borno dake Arewa maso dakarun tsaro na Operation HADIN KAI, bisa hadin gwiwa jami’an CJTF da mafarauta sun kai kai har hai kan mayakan boko haram a yankin Umbo Gen ranar a yammacin litinin a sumame karkashin OperationDesert Sanity IV.

Wata majiya ta shaidawa mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola cewa, dakarun sun afkawa mayakan boko haram a wani bata kasha da suka yi musayara wuta, abin da ya sanya suka sami nasarar hallaka 3 daga cikin su, yayin da wasu kuma suka guda da raunikan harbi a jukkunansu.

Sojojin sun sami nasarar kwato kayayyakin da dama da suka hadar da bindiga kirar AK47 da wayar hannun samfurin Itel, sai dai kuma kawo yanzu rundunar sojin kasar bata bayyana ko ta yi asarar rayukan sojojin ba.

A wani hari makamancin wannan dakarun runduna ta 6 karkashin shiyya ta 3 na dakarun Operation Whirl Stroke (OPWS) sun sami nasarar hallaka mayaka 2 a karamar hukumar takum dake jihar Taraba a wannan rana.

A wani atisaye, da dakarun suka gudanar bayan samun wasu sahihan bayanan sirri, dake cewa ýan ta’addan dake karkashin dabar Bojo, na shirin kai hari kauyen Chanchanji, wannan ne ya sanya dakaru tare su a hanyar Demeva zuwa chanchanji.

Arba tsakanin sojojin da ‘yan ta’addan ta sanya guda cikin ‘yan ta’addan ya mutu, yain da kuma wasu suka mutu a wata arba da aka sake yi a mashigar Demeva zuwa Gbudu.

Dakrun sojojin sun sami nasarar kwato bindiga kirara G3, da alburushi mai tsayin mita 7.62, babur mia kafa biyu. Sojojin kuma sun cigaba da sintiri a yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar dake rayuwa a yankin.

Haka kuma sojojin sun tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankunan Borno da Taraba da lamarin ya auku bisa cigaba da sintirin da dakarun sojojin ke yi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com