Hukumar tsaro ta DSS a Najeriya ta gurfanar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar Omoyele Sowore a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau, Talata, bisa zargin shi da aibata shugaba Bola Tinubu a shafinsa na X.
Hakazalika, DSS ta gurfanar da manyan kamfanonin sada zumunta na X da Meta a matsayin waɗanda ake ƙara.
Hukumar ta ce waɗannan kamfanoni sun ƙi goge abin da suka kira kalaman ƙarya da cin mutunci da aibata shugaba Tinubu da Sowore ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Tun a ranar 6 ga watan Satumban 2025 ne DSS ta sanar da cewa ta nemi a rufe ko a dakatar da shafin Sowore a dandalin X bisa zargin cewa yana yaɗa kalamai da za su iya haifar da rikici da barazana ga tsaron ƙasa.
Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin kare martabar shugabanci da kuma kare ƙasar daga mummunar tasirin yaɗa labaran ƙarya.
Hukumar ta bayyana cewa kalaman kai tsaye a kan Tinubu barazana ce ga tsaron ƙasar inda ta yi kira ga kamfanin X da ya goge tare da gaggauta rufe ko dakatar da shafin Sowore.
Amma kuma har yanzu X bai rufe shafin nasa ba inda DSS ta zargi kamfanin da rashin bin umarninta dalilin da ya sa ta gurfanar da kamfanin a gaban kotu.











