Abubuwan da Zan Cimma Idan na Zama Shugaban Kasa a 2023 – Gwamna Wike
Gwamnan jihar Ribas, ya bayyana abubuwan da yake so ya cimma idan ya zama shugaban kasa a zaben 2023.
Ya bayyana cewa, yana da yakinin dawo da zaman lafiya kasar nan matukar aka zabe shi domin ya gaje Buhari.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, Najeriya na bukatar shugaba kamarsa domin ciyar da kasar gaba da magance matsaloli.
Benue- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce da yardar Allah zai lashe zaben shugaban kasa na 2023 da aka sa a gaba.
Wike ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tuntuba da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP reshen Benue a gidan gwamnati da ke Makurdi a ranar Lahadi.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnan na jam’iyyar PDP ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karon farko a zabe mai zuwa, kamar yadda ya tada a Twitter.
Read Also:
Wike ya ci gaba da cewa, tare da jama’a za su aiwatar da wani tsari na hadin gwiwa don dawo da zaman lafiya da tsaro a ‘yan Najeriya.
Ya kuma sha alwashin magance matsalar rashin tsaro kwata-kwata a kasar matukar ya zama shugaba a 2023.
Ba Wike kadai bane dan jam’iyyar PDP da ya bayyana aniyar tsayawa takara a zaben mai zuwa ba.
Da yake amsa tambaya kan abin da zai yi na daban ga kasar nan idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, Gwamna Wike ya sha alwashin magance matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a kasar.
Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a filin jirgin sama na Kaduna a karshen mako, ya ce ‘yan Najeriya na bukatar shugaba mai daukar matakin gaggawa da zai magance matsalar rashin tsaro a kasar.
Da yake nasa jawabin, Wike ya bayar da tabbacin cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta samar da doka da oda domin a samu karin hannayen jarin kasashen waje kai tsaye zuwa kasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 3 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 44 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com