Yankin da Magajin Shugaba Buhari Zai Fito a 2023 – Gwamna El-Rufa’i
Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai ya ce APC na tsammanin ɗan takarar da zata tsayar ya fito daga kudancin kasar nan.
Gwamnan ya ce duba da kai kujerar shugaban jam’iyya arewa, suna tsammanin ɗan kudu ne zai gaji shugaba Buhari a 2023.
El-Rufai ya kuma zare kansa da maganar neman takara, amma ya ce idan Buhari ya nemi ya yi, to ba zai ƙi ba.
Abuja- Ana tsammanin ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe ƙarƙashin jam’iyyar APC zai fito ne daga yankin kudancin Najeriya.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ne ya yi wannan furucin ranar Laraba, yayin wata fira da Channels Tv.
Gwamnan ya yi bayanin cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa zai fito daga Arewacin Najeriya, dan haka suke tsammanin magajin Buhari ya fito daga kudu.
A kalamansa, El-Ruafa’i ya ce:
Read Also:
“Muna tsammanin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 zai fito ne daga wani wuri a yankin kudancin Najeriya.”
A cewar Malam Nasiru, ƙusoshin jam’iyyar APC a kudu ne zasu zauna su ga wane ɓangare daga yankinsu za su baiwa takarar.
Tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja ya ƙara da cewa, “Wuka da nama na hannun jiga-jigan APC na kudu su zakulo mana nagartaccen ɗan takara da za’a amince da shi.”
Shin APC zata iya kai bantenta a 2023?
Gwamna El-Rufa’i ya nuna kwarin guiwarsa da cewa APC zata cigaba da rike kujera lamba ɗaya a Najeriya, inda ya yi ikirarin cewa jam’iyyar na da duk abin da ake bukata na cigaba da mulki.
“Ina da yakinin a zaben 2023, APC zata lashe zaben shugaban ƙasa da kuma adadi mai yawa na kujerun gwamnoni.”
Gwamnan ya kuma zare kansa wajen shiga takarar wata kujera a zaɓe mai zuwa, amma yace zai iya fitowa takara matukar shugaba Buhari ya umarce shi da yin haka.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 38 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 20 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com