Gwamnan jihar Katsina ya ayyana dokar hana amfani da ‘yan daba a zaben 2023 mai zuwa nan da badi.
Ya bayyana hakan ne ta bakin mai ba shi shawari kan harkokin tsaro, ya kuma ba ‘yan siyasa shawari mai kyau.
Gamayyar kungiyar farar hula ta yabawa gwamnan, ta kuma bayyana kwarin gwiwar samun zabe na gari a Katsina.
Jihar Katsina – A kokarin tabbatar da zaben 2023 cikin aminci, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanya hannun kan dokar hana damawa da ‘yan daba a gangamin zabe a fadin jiharsa, AIT ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana wannan ne ta bakin mai ba shi shawari kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina, kuma ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaban shugabannin da suka dace a zaben da za yi.
Read Also:
Ya kuma bayyana cewa, tunda wannan ne zaben karshe da za a yi a mulkin Masari, yana da kyau a yi shi cikin aminci domin kafa tarihi na gari a jihar.
Hakazalika, ya ce gwamna Masari dattijon kasa ne, kuma zai tabbatar da zaman lafiya a jihar, musamman a kokarinsa na dawo da martabar jihar a matsayin kasa mai tarbar baki.
Ku dauki ‘ya’yan talakawa kamar naku, Masari ga ‘yan siyasa
Daga karshe ya shawarci ‘yan siyasa da suke yiwa ‘yan daba kallon ‘ya’yansu kuma ya kamata su ba su wadataccen ilimi a madadin bata rayuwarsu ta hanyar mai dasu tsageru.
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula ta CCSO, Abdulrahman Abdullahi ya yaba da kokarin Masari na damawa da ‘yan daba, tare da bayyana cewa hakan zai tabbatar da zabe na gari a Katsina.
Daga nan ne ya ce, idan gwamnati ta tabbatar da cikakken amfani da dokar, zai zama mafi alherin abin da gwamnan ya assasa.
Ko da a baya an taba jiyo yadda gwamnan ya yi irin wannan hani a watan Fabrairun 2022.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 17 hours 30 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 11 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com