Birtaniya ta janye gargadin da ta yi ga al’ummarta game da yiwuwar hare-haren ta’addanci a babban birnin Najeriya Abuja, inda ta ce a yanzu al’amura sun fara daidaita a birnin saboda daukar matakan kawar da waccan barazana da mahukuntan kasar suka yi.
Makwanni biyu bayan Ofishin jakadancin Birtaniyar ya bi sahun takwarorinsa na Amurka da Italiya wajen gargadin al’ummominsu da ke rayuwa a Najeriya kan su kauracewa ziyartar wasu sassa na kasar musamman birnin Tarayya Abuja game da yiwuwar hare-haren ta’addanci, Ofishin ya yi sake Magana da yayi tun da fari inda ya bayyana cewa yanzu barazanar ta kau a Abuja, sai dai har yanzu babu cikakken tsaro.
Read Also:
Wata sanarwar ofishin kula harkokin ci gaban kasashen renon Ingila na FCDO da ya wallafa a shafinta jiya litinin, ta ce ta janye batun hana al’ummominta bulaguro zuwa Abuja duk da cewa har yanzu akwai barazanar tsaron, sai dai ta ce har yanzu hanin ya na nan kan sauran sassan kasar musamman jihohin arewaci.
Ofishin na FCDO ya sabunta gargadi kan ziyarta jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da kuma Katsina baya ga Zamfara da Delta, da Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom da kuma Cross River wadanda Ofishin ya ce suna fama da barazanar hare-haren ta’addanci .
Sanarwar ta ce bata sauya zani ba, game da barazanar hare-haren ta’addancin da ake fuskanta a jihohin Bauchi da Kano da Jigawa da Neja da Sokoto da Kogi State baya ga wani yanki na jihar Kebbi mai tazarar kilomita 20 da jihar Neja kana jihar Abia sai kuma wasu sassa na jihohin Delta da Bayelsa da Rivers da Pulato da Taraba.
Ofishin ya shawarci matafiya da su rika duba sanarwar hukumomi game da yanayin tsaron yankin kafin kai ziyara yayinda yace mafi dacewa shi ne al’ummomin na Birtaniya su kaucewa zuwa jihohin haka zalika su yi taka-tsan-tsan da ratsawa wata kasa a kokarinsu na komawa gida.
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 22 minutes 52 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 4 minutes 17 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com