Ana cigaba da bincike kan rikicin daya haddasa mutuwar akalla mutane 20 cikin makon nan a rikicin kabilancin da ke ci gaba da tsananta tsakanin kabilar Yaka da Teke na lardin Mai-Ndombe a Mahukuntan Jamhuriyar Demokradiyar Congo.
Tsawon watanni ana fama da rikicin kabilancin a yankin Mai-Ndombe inda alkaluman gwamnatin kasar ke cewa daga faro fadan a watan Yunin da ya gabata zuwa yanzu an kashe fararen hulan da yawansu yah aura 180 ciki har da wasu 16 a makon jiya kari kan mutane 20 da aka kashe a cikin makon nan.
Majiyoyi daga yankin sun ce rikicin ya faro bayan takaddama game da biyan haraji lamarin da zuwa yanzu ya tilasta dubunnan mutane daga kabilun biyu na Yaka da Teke tserewa daga yankunansu don tsira da rayukansu.
Read Also:
Duk da cewa kamfanin dillancin labaran Faransa ya gaza tattara hakikanin alkaluman mutanen da rikicin ya daidaita da kuma wadanda suka mutu, amma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa matukar ba a dauka matakan da suka kamata ba, rikicin ka iya juyewa zuwa mafi muni.
Rahotanni sun ce a litinin din da ta gabata ne, wasu maharan kabilar Yaka rike manyan bindigu suka farwa kauyen Teke lamarin da ya sanya al’ummar garin kare kansu ta hanyar daukar makamai inda nan take akayi asarar rayukan mutane akalla 20.
Wani ganau a yankin na Teke, Nkete Mboma Butu y ace adadin mutanen da suka mutu ka iya zarta alkaluman da mahukuntan kasar suka bayyana la’akari da yadda aka samu asarar rayuka daga dukkanin bangarorin biyu.
Da ya ke bayar da bahasi kan rikicin na makon nan yayin jawabinsa gaban wakilan gwamnati a Kinshasa mataimakin shugaban yankin Moise Makami Muzik ya ce alkaluman mutanen da suka mutu a rikicin ya haura 35.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 22 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 3 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com