Wani labari na yawo a kafafen sada zumunta na zamani cewa hukunar FIFA zata ajje kafafun Pele a gidan tarihi.
Cikakken Labarin: Wallafar tace Yanzu Yanzu: “FIFA zata Ajje
Kafafun Pele a gidan Adana kayan Tarihi, kuma iyalensa Sun Amince.”
FIFA hukumar kwallon kafa ce da aka samar da ita a shekarar 1904.
Shi kuwa Pele wato, Edson Arantes do Nascimento, wanda aka fi sani da Pele dan kasar Brazil ne, kuma hamshakin dan wasa daya bawa kasar muhimmiyar gudunmawa ga tawagar kasar, wanda kuma ke da muhimmanci ga hukumar ta FIFA. Kuma guda cikin wadanda suka sami gagarumar nasara cikin ‘yan wasan karni na 20 a kasar sa.
Suna kiransa da Sarki, kuma fuskar sa na cikin fuskokin da aka fi ganewa a duniyar kwallon kafa. FIFA ta ambace shi da dan wasa mafi daraja a karni na 20.
Hamshakin dan wasan na tawagar Brazil ya mutu a ranar 29 ga watan Disambar 2022.
Tauraruwar Pele ta fara haskawa tun yana dan shekaru 17 a duniya, lokacin daya sami nasarar lashe gasar cin kofin duniya da aka gudabar a kasar Sweden a ranar 29 Yunin 1958.
Ya juma cigaba da rike kambunsa na mafi kankantar shekaru a duniya.
Gaskiyar Labarin: Bayan gudanar da bincike a kafar Intanet, ya bamu sami wani labari dake da alaka ta kusa ko ta nesa da wannan labarin ba daga kafar yada labarai sahihiya.
Haka kuma shafin da aka samar domin karbar gaisuwar mutuwar Pele ba sanar da wannan labarin ba.
Haka kuma mun bincika shafin hukumar ta FIFA musamman shafukan twitter, Instagram babu wata sanarwa makamanciyar wannan.
Sai dai wasu tashoshi a dandadin YouTube da twitter sun tabbatar da labarin tare da yada shi.
A Takaice: babu wata sanarwa daga hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, dake cewa za’a Ajje Kafafun Pele a gidan tarihi kuma iyalen sa sun Amince.
Dan haka PRNigeria ta tabbatar da cewa labarin nan ba gaskiya bane ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 2 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 44 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com