Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje bisa Samar da asibitin Masu fama da cutar daji a jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya.
Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake bude asibitin dake unguwar giginyu a karamar hukumar Nasarawa ta jihar kano.
Buhari yace dole a ya yabawa hangen nesa na gwamna Ganduje na samar da Asibitin Saboda yadda zai taimaka wajen magance fita waje domin neman lafiya da Kuma bunkasa tattalin arzikin Nigeria.
A nasa jawabin gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce an samar da Asibitin ne don rage yawan fita kasashen waje domin neman lafiya.
Yace asibitin shi ne irinsa na farko a Nigeria da Africa baki daya, Kuma zai bunkasa tattalin arzikin jihar kano da kasa baki daya.
An dai sanyawa Asibitin sunan Mai dakin gwamnan kano Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje.
Bayan nan Shugaba Buhari ya bude katafariyar Gadar dake Hotoro wacce aka Saka mata sunan Muhammadu Buhari, da gidajen gwamnatin tarayya dake Darmanawa da Kuma Cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote dake kan titin Zaria da dai sauran su.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1246 days 22 hours 38 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1229 days 20 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com