Majalisar tsaron Najeriya da shugaban Buhari ya jagoranta ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, kamar yadda aka tsara.
Babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a na ƙasar Abubakar Malamin ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar a fadar shugaban ƙasar.
Read Also:
Malami ya ce babban hafsan tsaro na ƙasar Janar Lucky Irabor, da hafsoshin rundunonin sojin ƙasar uku tare da babban sifeton ‘yan sandan ƙasar sun yi wa majalisar bayani game da shirin da suka yi kan babban zaɓen da ke tafe ranar Asabar mai zuwa.
Ya ƙara da cewa ”dangane da haka, majalisar ta haɗu a kan cewa zaɓen na ranar Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara”.
Taron ya zo ne bayan, da taron majalisar magabata ta tabbatar da shirin hukumar zaɓen ƙasar da na ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a kan zaɓen na ranar Asabar mai zuwa.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 16 hours 55 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 18 hours 36 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com