Akalla hare-hare 60 aka kai tare kuma da kashe mutum tara a lokacin yakin neman zaɓe a faɗin Najeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya da za a gudanar a ranar Asabar.
Cibiyar Tabbatar da Dimokuraɗiyya da Ci Gaba CDD, ce ta bayyana hakan a cikin wani rahoto da ta fitar gabanin shiga rumfunan zabe domin kaɗa kuri’a, inda ta ce wasu da dama kuma sun jikkata a hare-haren da aka kai tun fara yakin neman zaɓe a watan Satumban 2022.
CDD ta ce batun rashin tsaro da ƙarancin man fetur da na kuɗi da kuma sauran abubuwa za su iya kawo cikas ga yadda zaɓen zai gudana.
Read Also:
“A karshen shekarar 2022, rikice-rikicen da ke da alaƙa da siyasa sun ƙaru tun bayan zaɓen 2019 da aa gudanar. Alkaluman da muka tattara ya nuna cewa an kai hari sau 60 a lokacin yakin neman zaɓe, inda mutum tara suka mutu,” in ji CDD.
Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda ta ce ‘yan siyasa na ɗaukar ‘yan bangar siyasa domin kawo cikas a zaɓen da za a gudanar, inda ta ce hakan zai ƙara janyo taɓarɓarewar matsalar tsaro.
Cibiyar ta yi kira jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cewa mambobin da kuma magoya bayansu sun bi sahun sharuɗan da aka kwamitin zaman lafiya ya zartas yayin lokacin saka hannu a yarjejeniyar yin zaɓe lami lafiya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 7 hours 21 minutes 13 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 9 hours 2 minutes 38 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com