Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta ce ambaliyar ruwa ta raba dubban mutane da muhallansu a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.
wannan na cikin wata sanarwa da hukumar ta NEMA ta wallafa a shafinta na X, in da ta ce ambaliyar da ta faru ranar Litinin ta shafi garuruwa kusan 20 a ƙananan hukumomin Shagari da Tureta.
“Ruwan ya shafe gadar da ke haɗa Shagari da Tureta baki ɗaya kuma ya hana mutane zirga-zirga a yankin,” a cewar sanarwar.
“Haka nan ambaliyar ta shafi ayyukan noma, inda ta shafe gonaki da dama.”
ko dai a ‘yan tsakanin nan Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin samun ambaliyar a wasu jihohin ƙasar sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu kwanan nan.
Hukumar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa.
ko da yake dai hukumar bata ambaci jihar Sokoto a cikin jerin jihohin da zasu iya samun ambaliyar ba, ko da yake ta bukaci suaran al’umma dasu dauki matakin da suka dace wajen gyara magunan ruwan su tare da kaucewa yin gini akan hanyar ruwa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 41 minutes 18 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 22 minutes 43 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com