Majalisar Ɗinkin Duniya ta bai wa mutanen da ambaliyar Maiduguri ta shafa tallafin dala miliyan shida.
Wata sanarwa da ofishin jami’in kula da ayyukan jin kai a Najeriya, Mohammed Fall ya fitar, ya ce haɗin gwiwar ƙungiyoyin agaji na MDD da masu zaman kansu, ciki har da Red Cross, sun kai ziyara birnin Maiduguri a karshen mako.
A cewarsa, tawagar ta haɗu da mutanen da abin ya shafa – waɗanda yawanci rikicin Boko Haram da kuma rashin tsaro ya riga ya ɗaiɗaita.
“Mu tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi na samar wa da mutanen kayan abinci, muna kuma jefa musu abinci ta sama a wuraren da ke wahalar kai wa, har ma da ruwan sha,” in ji shi
Ya kuma ce suna kula da lafiyar waɗanda aka tsugunar a sansanoni musamman ma mata da yara mata da kuma tabbatar da cewa ba a samu ɓarkewar cutuka ba.
Ambaliyar ta afku ne bayan fashewar madatsar ruwa ta Alau wanda ke nisan kilomita goma da kudancin Maiduguri.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 10 hours 59 minutes 10 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 40 minutes 35 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com