Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na baƙin ƙoƙarinta wajen lalubo hanyoyin magance rikice-rikicen manoma da makiyaya.
Yayin da yake jawabi bayan sanya hannu da wasu kamfanin sarrafa nama na JBS a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil, Shugaba Tinubu ya ce rikicin manoma da makiyaya ya jima yana haifar da asarar dukiyoyi a wasu yankunan Afirka.
”Rikici tsakanin manoma da makiyaya da ke haifar da asarar rayuka da zubar da jini, idan aka yi amfani da dabarun zamani da wayewa wajen magancenta, zai kawo ci gaban tattalin arzikinmu”, in ji shugaban ƙasar.
Read Also:
Bayan ƙulla yarjejeniyar kamfanin sarrafa nama na JBS ya amince da zuba jarin dala miliyan 2.5 domin gina kamfanonin sarrafa nama shida a faɗin Najeriya.
Kamfanin ya ce uku daga cikin kamfanonin za su mayar da hankali wajen sarar naman kaji, ayayin da biyu za su sarrafa jan nama, sai kuma guda wanda zai sarrafa nama aladu.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen gayyato masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasar a ɓangaren kiwon dabbobi da noma, lamarin da ya ce zai taimaka wajen magance rikici tsakanin manoman da makiyaya, tare da yaƙar yunwa da talauci da inganta ci gaban tattalin arziki.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 2 hours 27 minutes 23 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 4 hours 8 minutes 48 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com