Hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Najeriya NHRC ta sanar da karɓar ƙorafe-ƙorafen take haƙƙin ɗan adama har dubu 3 da 19 tsakanin watan Janairu zuwa Disamban shekarar da ta gabata a jihar Kano kaɗai.
Cikin ƙorafe-ƙorafen da ke gaban hukumar masu alaƙa da cin zarafin mata da ƙananan yara su ne kan gaba a jihar ta Kano, kamar yadda alƙaluman hukumar ke nunawa.
Shugaban hukumar a jihar ta Kano Shehu Abdullahi da ke sanar da hakan ga manema labarai a yau Litinin ya ce cikin ƙorafe-ƙorafen fiye da dubu 3 da aka gabatar gabansu sun yi nasarar magance dubu 2 da 276.
Shugaban hukumar ta NHRC a Kano, ya kuma ce yanzu haka hukumar na aiki kan ƙorafe-ƙorafe 743 da basu kai ga kammala warwarewa ba.
Read Also:
A cewar shugaban na NHRC galibin ƙorafe-ƙorafen da aka fiya miƙa musu a jihar ta Kano sun fi shafar batutuwa masu alaƙa da watsi da baiwa yara kulawa, ko kuma take haƙƙin yaran, kana cin zarafi a cikin gidajen aure sai take haƙƙin zamantakewa ko na rayuwa sai kuma batutuwa masu alaƙa da al’adu da zamantakewar iyali.
Shugaban na NHRC ya ce sauran ƙorafe-ƙorafen da hukumar ke samu sun shafi cin zarafi daga jami’an tsaro, cin zarafi ta hanyar lalata musamman ga mata kana matsalar iyaye ta rashin ɗaukar nauyin iyalansu da sauran ƙorafe-ƙorafe masu alaka da rayuwar yau da kullum.
Shugaban hukumar kare haƙƙin bil’adaman ta Najeriya rashen jihar Kano Abdullahi Shehu ya sha alwashin ɗaukar gaɓarar fara aikin wayar da kan jama’a hatta a yankunan karkara ciki har da shirya taruka na musamman don ankarar da jama’a kan haƙƙoƙinsu.









