Shugaban (NITDA) ya Halarci Taron Karrama Mai Girma Gwamnan Jigawa:-
Mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), a yau ya halarci taron karrama mai girma gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, (MON, MNI), wanda ƙungiyar cigaban ƙasar Haɗejia, (Haɗejia Ina Mafita Initiative) ta yi.
Taron ya samu halartar mai girma mataimakin gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Ɗan Moɗi, da mai girma kakakin majalissar dokoki na Jihar Jigawa, Onarabul Idris Garba Kareka, da mai martaba sarkin Haɗejia, kana kuma shugaban majalissar sarakunan Jihar Jigawa, Dakta Adamu Abubakar Maje Haruna, (CON), da mai girma sanatan ƙasar Haɗejia, Barista Ibrahim Hassan Haɗejia, (Shatiman Haɗejia Na Biyu), da mai girma tsohon shugaban hukumar kula da shige da fice ta ƙasa, (NIS), Alhaji Muhammad Babandede,
Read Also:
Sai kuma ƴan majalissar wakilai na tarayya da ƴan majalissar dokokin Jiha, da shugabannin ƙananan hukumomi da sauran muhimman mutane da dama na ƙasar Haɗejia da Jigawa.
Daga bisani kuma kafin ya komawa birnin tarayya, Abuja, mai girma shugaba ya karɓi baƙuncin al’umma daban-daban, dattawa, matasa, da kuma ƴan ƙungiyoyi, waɗanda su ka haɗa da: ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyi magoya bayan shugaban ƙasa Malam Muhammadu Buhari, (GCFR), “Coalition Of Buhari Support Groups”, (COBSG), ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Onarabul Musa Gambo Guri, waɗanda su ka kai masa ziyarar girmamawa tare da godiya a bisa wakilci da ya aike wurin babban taron ƙungiyar na shiyar Arewa Maso Yamma da aka yi a Jihar Jigawa.
Kana kuma, ya karɓi baƙuncin wasu daga cikin matasan da su ka samu horo kan ilimin gyaran wayar salula da sauran harkokin fasaha na zamani wanda hukumarsa ta gudanar a kwanan nan, inda su ka ziyarce shi domin yi masa godiya da yabawa kan ƙoƙarin da ya ke wajen ɗora rayuwar matasa kan harkar cigaba domin bunƙasa cigaban ƙasa da duk al’umma.
Lahadi, 6 ga watan Janairu, 2022.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 12 hours 1 minute 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 42 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com