Majalisar Dattawa ta yi Watsi da Kudurin Dokar Zabe da Shugaba Buhari ya Gabatar
Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudurin dokar zabe da shugaba Buhari ya gabatar saboda wasu dalilai.
A baya majalisar ta fusata da jin yadda kotu ta ba da umarni gareta cewa, kada ta sake ta gyara dokar zaben.
A yau dai majalisar ta kawo karshen magana, ta kada kuri’a kuma an yi watsi da dokar gabanin karatu na biyu.
FCT, Abuja – Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, majalisar dattawa a ranar Laraba ta yi watsi da kudirin doka da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar na neman gyara dokar zabe ta 2022.
Kudirin doka mai taken: “Kudirin dokar da zai gyara dokar zabe ta 2022 da kuma abubuwa masu alaka, 2022,” Sanatoci sun yi watsi da shi, lamarin da ya dakatar da karatun kudurin na biyu.
Read Also:
Kudurin dokar ya tsallake karatu na farko a ranar Talata duk da umarnin da kotu ta bayar na hana Majalisar Dattawa yin aiki akansa.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya kalubalanci hukuncin kotun yana mai cewa a kowane hali, bangaren shari’a bai da ikon hana majalisar gudanar da ayyukanta na tsarin mulki.
Kafin Majalisar Dattawa ta fara nazarin kudirin a ranar Laraba, Sanata Adamu Aliero, yayin da yake karanto doka ta 52 (5) na Majalisar Dattawa, ya bukaci Shugaban Majalisar da ya yi watsi da shawarar duba ga kudirin.
Sai dai Lawan ya dage. Ya sake jaddada matsayinsa na cewa Sanatoci ne ke da hakkin kin amincewa da kudirin ba bangaren shari’a da ke neman hana majalisar gudanar da ayyukanta ba.
Saboda haka, Sanatoci sun kada kuri’ar kin amincewa da kudirin na hana sake karanta shi a karo na biyu.
Karin bayani na nan tafe…
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 52 minutes 20 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 33 minutes 45 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com